An binne gawar marigayi Tsohon Gwamnan jihar Oyo Abiola Ajimobi a gidansa da ke Olu-wole a birnin Ibadan bisa koyarwar addinin Musulunci.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa an yi jana’izar marigayin a ranar Lahadin nan, cikin tsauraran matakan tsaro bisa dokokin da aka shimfida na hana yaduwar cutar corona.
Kafin rasuwar marigayin ya kasance shi ne Shugaban Jam’iyyar Apc a sashen kudu maso yammacin kasar Nijeriya.
Ya rasu ne a wani asibiti ne mai zaman kansa da da ke birnin Legas sakamakon harbuwa da cutar corona.
