Home Kasashen Ketare An yi sauye-sauye a majalisar zartaswar Nijar

An yi sauye-sauye a majalisar zartaswar Nijar

230
0

Yakuba Umaru Maigizawa

A ranar Litinin ne gwamnatin jamhuriyar Nijar ta gudanar da wani dan kwarya-kwaryan garambawul a cikin gwamnatinta.

Sakataren gwamnatin kasar Malam Abdourahaman Zakaria ne ya karanta sanarwar a kafar talabijin ta kasar da ta ce garambawul din ya shafi ma’aikatun gwamnatin ne har guda shida (6). Sai dai ciki wanda ya fi daukar hankali shi ne na canza ministan cikin gida malan Bazoum Mohamed wanda kuma shi ne dan takarar shugabancin kasar na jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulki.

Dama dai an jima jam’iyyu adawa da kungiyoyin farar hula na kira ga gwamnatin da ta sauke dukkan wasu da za su tsaya takarar shugabancin kasar daga mukamin minista kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply