Home Labarai An yi sulhun manoma da makiyaya a Kebbi, an hana makiyaya kiwon...

An yi sulhun manoma da makiyaya a Kebbi, an hana makiyaya kiwon dare

29
0

Masarautar Argungu da ke jihar Kebbi ta gudanar da taron sulhu tsakanin manoma da makiyaya a kokarin samar da dauwamammen zaman lafiya.

Alhaji Ibrahim Hassan Kwaido, Kundudan Kabi ya bayyana cewa sun yanke shawarar daukar wannan mataki ne saboda yadda manoma suka dukufa ga noman rani don gudun kada makiyaya su afka gonakin su.

Shi ma mai martaba Sarkin Kabin Argungu a cikin yarjejeniyar, ya ja kunnen manoma akan kada su tattare burtula da hanyoyin da makiyaya ke bi don ciyar da dabbobin su.

Sannan, an haramata wa makiyaya kiwo bayan karfe 8 na dare.

Dukkanin bangarorin biyu na makiyaya da manoma sun amince da kulla yarjejeniyar don samun nagartaccen zaman lafiya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply