Home Coronavirus An yi wa Paparoma rigakafin Covid-19

An yi wa Paparoma rigakafin Covid-19

46
0

Paparoma Francis, mai shekara 84, ya karbi rigakafin cutar coronavirus a ranar Laraba, kamar yadda rahotanni daga kafofin yada labaran kasashen waje suka tabbatar.

Wata jaridar yanar gizo mai suna Jesuit da ke kasar Amirka, da kuma La Nacion, ta kasar Ajantina sun rawaito labarin yadda aka yi wa Paparoma rigakafin.

A ranar Lahadin da ta gabata, Paparoman ya bukaci mutane su karbi allurar rigakafin Covid-19, a lokacin da yake wata hira da gidan talbijin na kasar Italiya Canale 5.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply