Home Labarai An yi wa sabon shugaban EFCC karin girma

An yi wa sabon shugaban EFCC karin girma

40
0

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta yi karin girma ga shugabanta na riko, Abdulrasheed Bawa da wasu jami’an hukumar 88.

Karin girman da aka yi wa sabon shugaban hukumar ta EFCC ya zo ne kasa da mako guda bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ayyana sunansa a matsayin wanda zai maye gurbin Ibrahim Magu da aka dakatar sakamakon tuhumar da ake yi masa.

Wata majiya daga hukumar ta EFCC ta fada wa jaridar PRNigeria cewa karin girman da aka yi wa sabon shugaban hukumar ta EFCC ya yi dai-dai da matsayin mataimakin kwamishinan ’yansanda, ACP, matsayin da zai sanya shi cancantar shugabancin hukumar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply