Home Labarai Karanta abin da ya faru da Rarara a Katsina

Karanta abin da ya faru da Rarara a Katsina

776
0
Mawaki Rarara tare da jarimi Ali Nuhu
Mawaki Rarara tare da jarimi Ali Nuhu

Rahotanni sun ce an yi wa tawagar mawakin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara ihu a Katsina a lokacin da suke daukar sabuwar wakarsa mai suna ‘JIHATA’ ta rashin tsaro a jihar.

Wani shaidar gani da ido ya DCL Hausa cewa Rarara da abokan aikinsa irinsu Ali Nuhu, Abubakar Mai shadda, Tijjani Asase tare da sauran ma’aikatan da suke aikin shirin wakar mai mintuna 32:22, sun kammala abin da ya kai su a kasuwar “Central Market” Katsina, har sun tafi, sai wasu da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne suka fara yi wa ayarin ihu.

Mawaki Dauda Rarara
Mawaki Dauda Rarara

Bayanai sun ce matasan sun yi musu ihun cewa “Karya ne, ba ma yi”, ba ma so, ‘dan yaudara ne miyar gidansa ya ke gyarawa ba kare talaka ya ke ba”.

Rahotanni sun ce har an fasa masa danjar motar ayarin a lokacin yamutsin duk kuwa da cewa akwai jami’an tsaro tattare da su.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply