Home Sabon Labari An yi waje da Kano Pillars a gasar zakarun Afirka

An yi waje da Kano Pillars a gasar zakarun Afirka

68
0

Sharifudeen Ibrahim Muhammad/Banye

Kano Pillars ta kasa tsallakewa zuwa zagaye na gaba a gasar cin kofin zakarun Nahiyar Afrika.
Ƙungiyar ta kasa tsallakewa zuwa mataki na gaban ne, biyo bayan rashin nasara da suka yi a hannun ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ashante Kotoko ta birnin Kumasi na ƙasar Ghana da ci 2-0 a wasan da aka fafata a filin wasan Baba Yara.

A wasan farko dai da aka buga a filin wasa na Sani Abacha da ke Kanon Nijeriya, Kano Pillars ce ta yi nasara da ci 3-2 wanda jimillar wasan ya kasance Kotoko na da ci 4 Pillars na da 3.

Pillars wadda ake wa laƙabi da ‘Masu gida’ na buƙatar aƙalla kunnen doki da zai ba su damar tsallakewa zuwa zagaye na gaba, wanda hakan bai samu ba. Yanzu haka dai ƙungiyar Enyimba ce kaɗai ta rage a cikin ƙungiyoyin da ke wakiltar Nijeriya a gasar zakarun ta Afrika ta shekarar 2019-20.

Hakan ya biyo bayan nasarar da ta yi kan ƙungiyar Pummeled Rahimo ta ƙasar Burkina Faso da ci 5-0 a wasan da a ka buga a filin wasan ƙungiyar na birnin Aba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply