Home Labarai An yi wa wasu manyan hafsoshin soji sauyin wurin aiki

An yi wa wasu manyan hafsoshin soji sauyin wurin aiki

214
0

Rundunar sojin Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Laftanal Tukur Yusuf Burutai ta amince da sauya wa manyan hafsoshin soji kimanin 34 dama wasu masu mukamin Kanal 5 wuraren aiki.

Rundunar ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin Babban Daraktan hudɗa da jama’a na rundunar Kanal Sagir Musa.

Sai dai sanarwar ta ce sauyin wajen aikin zai fara aiki ne daga ranar 20 ga watan Yulin nan da muke ciki.

Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar ta gudanar da wannan sauye-sauyen ne domin a ƙara inganta tsarin yadda ake aiwatar da ayyukan rundunar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply