Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Ana ƙara samun masu sayen hannun jari a AfBD – Adesina

Ana ƙara samun masu sayen hannun jari a AfBD – Adesina

148
0

Bankin raya nahiyar Afrika ya janyo hankalin masu sayen hannun jari, inda suka zuba adadi mafi yawa cikin shekaru biyu.

Shugaban bankin Mista Akinwumi Adesina ya bayyana haka jim kaɗan bayan ya amshi rantsuwar kama aiki na ƙarin wa’adin shekaru 5.

Adesina ya ce an sayi hannun jari da darajar kuɗaɗensa suka kai dala milya dubu 79 a cikin shekaru biyu.

Ya ƙara da cewa ƙasashe da dama suna ci gaba da cin moriyar bankin, kuma yanzu haka bankin ya ƙara zaƙulo wasu ƙasashe guda 44 a nahiyar da za su ƙara ƙarfafa hudɗa da shi ciki har da da ƙananan ƙasashen da karan su bai kai tsaiko ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply