Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Ana bin kowane dan Nijeriya bashin N155,000

Ana bin kowane dan Nijeriya bashin N155,000

190
0

Ofishin Kula da basuka na kasa (DMO) ya ce yawan basukan da ake bin Nijeriya ya karu zuwa tiriliyan 31 a watan Yuni, 2020.

Ana ganin yawan bashin zai karu a bana saboda rancen da za a karbo daga hukumomin kasashen duniya.

Zuwa watan Maris 2020, bashin ya kai tiriliyan N28.6 wanda ya kunshi dukkannin basukan Gwamnatin Tarayya, Jihohi da Birnin Tarayya.

Jaridar Aminiya ta rawaito cewa a baya-bayan nan yawan bashin ya kai tiriliyan N31.009 ya kai Dala biliyan 85.897, yayin da tiriliyan N28.628 na watan Maris ya kai biliyan N79.303.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply