Home Labarai Ana bin matakan kariyar corona a wurin jarabawar WAEC a Katsina?

Ana bin matakan kariyar corona a wurin jarabawar WAEC a Katsina?

148
0

Hukumomi sun sanar da ranar 17 ga watan Agusta 2020 a matsayin ranar fara zauna jarabawar karshe ta WAEC ga daliban sakandare.

Bullar cutar corona ne dai ya jaza har jarabawar ta kai watan na Agusta ba a fara zauna ta ba.

To sai dai kamar yadda kwamitin yaki da cutar corona na Nijeriya ya sanar, za a rika gudanar da jarabawar ne a cikin matakan kariya daga cutar corona.

Matakan kamar yadda kwamitin ya zayyana, sun hada da kauce wa cudanya, saka takunkumin hanci, tanadar wuraren wanke hannu da sauran matakan kariya daga cutar.

Sai dai babu tartibin bayani daga ma’aikatar ilmi ta jihar Katsina na ko an samar da isassun kayan kariya daga cutar corona ganin yadda ake samun tsambare na wasu dalibai da ke zauna jarabawar amma babu takunkumin rufe hanci, kuma duk sun cude a wasu makarantun.

Wasu daliban sakandire
Wasu daliban sakandire

Wasu iyaye a jihar Katsina da DCL Hausa ta zanta da su, sun nuna damuwarsu da kurarren lokacin da aka saka na fara zauna jarabawar.

Malam Yusuf Adali, ya ce “ka ga an dade zaune a gida babu makaranta, babu bita kuma ga shi yaranmu ba a yi musu darasi na musamman, ta ya za su zauna wannan jarabawar kuma a ce so ake su yi nasara”.

Wata daliba da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce “wannan lamari, sai dai mu tattara mu mika wa Allah, amma dai cin wannan jarabawa akwai aiki”.

Masu sharhi kan lamurran yau da kullum, na ganin da a ce ba a zauna jarabawar ba gaba daya, gwara a yi ta ko a halin kaka, don kada jadawalin karatu na shekarar ya lalace.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply