Wani kwararre a fannin kiwon lafiya ya ce Nijeriya na bukatar karin nas-nas da ungozoma 800,000 domin su iya kula da yawan jama’ar kasar milyan 200.
Shugaban kungiyar nas-nas da umgozoma na kasa Adeniji Abdrafiu ya ce yawan wadannan jami’an ne hukumar lafiya ta duniya ta amince da shi.
Ya ce ya zuwa yanzu, akwai rauni ta fuskar yawan nas-nas da sauran malaman kula da lafiya.
