Home Labarai Ana bukatar milyan 81 don sassaben ciyawa a babban filin wasa na...

Ana bukatar milyan 81 don sassaben ciyawa a babban filin wasa na Abuja

258
0

Ministan wasanni na Nijeriya Sunday Dare yace an mika wa gwamnatin tarayya kiyasin Naira milyan 81 don gudanar da aikin sassabe ciyawar babban filin wasa na Abuja.

Sunday Dare ya furta hakan ne a shafinsa na twitter. Sai dai yace ma’aikatar wasanni ba ta da isassun kudaden da za a gudanar da wannan aiki.

Ministan yace hankali ma ba zai dauka ba, idan aka ce an kashe Naira milyan 81 wajen sassaben ciyawa kadai.

Punch ta rawaito cewa ma’aikatar wasanni da matasa ta yi kiyasin kasafin kudi na Naira milyan 798 don gudanar da ayyuka daban-daban a filin wasan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply