Home Labarai Ana Bukatar N68bn don bada tallafin abinci a Nijeriya – Rahoto

Ana Bukatar N68bn don bada tallafin abinci a Nijeriya – Rahoto

125
0

A cikin wani rahoto da shirin samar da abinci na majalisar dinkin duniya ya fitar, ya ce ana bukatar Naira Biliyan 68 domin ci gaba da aikin bada tallafin rayuwa da ake yi a Nijeriya har na tsawon watanni shida masu zuwa.

Babbar mai magana da yawun shirin Elisabeth Byrs, wadda ta bayyana haka, ta ce ana bukatar tallafin kudin cikin gaggawa domin taimakawa mutanen da cutar coronavirus ta fi yiwa illa.

Ta ce daga cikin mutanen akwai wadanda rikicin Boko Haram ya shafa a jihohin Adamawa, Borno da Yobe da ke Arewa maso Gabas.

Rahoton ya kuma ce akalla mutane miliyan 3.8 ne, wanda yawanci ke aiki a kamfanoni ke fuskantar barazanar rasa ayyukan su, a daidai lokacin da ake tunkarar mayuwacin hali na barkewar cutar Covid-19.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply