Home Kasashen Ketare Ana ci gaba da rajistar mallakar katin zabe a Nijar

Ana ci gaba da rajistar mallakar katin zabe a Nijar

88
0

A ranar asabar kin nan ce da ta gabata ta 8 ga watan Feburairu aka kaddamar da fara aikin rajistan ‘yan kasa da suka cancanci kada kuri’a a zabe mai zuwa a yanki na biyu wato zone 2

Yankin dai na biyu ya kunshi jihohi hudu(4) ne na kasar da suka hada da Damagaram, Diffa, Maradi da kuma babban birnin Yamai

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan kamalla aikin rajistan a yanki na farko zone1 da ya shafi wasu jihohin hudu

Ya zuwa yanzu dai rahoanni daga yankunan na jihohin da ake gudanar da wannan aiki na cewa babu wata matsala da ake fuskanta kuma al’umma na fitowa dafifi wajen zuwa a masu rajistar

A zagayen da jaridar DCL Hausa ta yi a wasu cibiyoyin masu rajistar na birnin Damagaram ta lura cewa mata da matasa su suka fi fitowa dan yin rajistar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply