Home Labarai Ana ci gaba da samun koke-koken cin zarafin mata da kananan yara...

Ana ci gaba da samun koke-koken cin zarafin mata da kananan yara a Nijeriya-Cibiya

72
0

Hannatu Mani Abu/Jani

Cibiyar dake kare wadanda a ka ci zarafi a Kaduna ta karbi koke-koken cin zarafin mata da kananan yara akalla dari shidda da sattin da biyu(662) tun bayan kafa ta a 2016.

Isa Ibarahim wani mai bada shawara na kare hakkin yara a kumgiyar da ke kare hakkin kananan yara ta “Save The Children a Kaduna ya bayyana cewa an shirya taro na musamman da nufin jan hankalin alumna domin tallafa wa wajen kare hakkin yara da cin zarafinsu ta wajen kai rahoton cin zarafin yara a cibiya mafi kusa.

Ibrahim ya ce cibiyar na duba lafiyar wadanda abin ya shafa tare da yin juyayi ga iyalan da abin ya shafa.

Da ta ke tofa albarkacin bakinta, shugabar cibiyar kare cin zarafin yara ta Salama Mrs Grace Yohanna ta ce cibiyar na tallafawa da magunguna da kuma daukar matakan da suka dace a bangaren shari’a.

Mrs Grace ta yaba wa gwamnatin jihar Kaduna da ta samar da ire-iren cibiyoyin ta kuma ce cibiyoyin na da bukatar magunguna ta kuma mika kokon bara ga al’ummomi domin kai duk wani rahoton cin zarafin yara. Ta ce mata ne wadanda suka fi samun matsalar cin zarafi.

Mr Denis Onoise mai rajin kare hakkin yara da ke aiki da Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya _UNICEF_ ya bayyana cewa yawancin ma su cin zarafin yara ba baki bane mutane ne na kusa-kusa, kamar iyaye da kawunnai da malamai da sauran yan uwa.

Onoise ya ce wani bincike da hukumar tantance yawan jama’a tayi da tallafin Asusun _UNICEF_ a shekarar 2014 ya bayyana cewa Nijeriya ce kan gaba wajen cin zarafin yara kanana.

Daga karshe yayi kira ga iyaye da su kula da yaransu tare da kai rahoton abin da ya shafi cin zarafi ga hukumar da ta da ce.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply