Home Labarai Ana gab da sakin kamammun Neja – Gumi

Ana gab da sakin kamammun Neja – Gumi

36
0

Shaihin malamin nan mai da’awar addinin musulunci Ahmed Gumi ya tabbatar da cewa ba da jimawa ba za a saki daliban Kagara da aka yi garkuwa da su a jihar Neja.

Ya bayyana hakan jim kadan bayan ganawa da ƴanbindigar a dajin da ke tsakanin Tagina da Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Wani da ya shaida faruwar lamarin ya ce, Sheikh Gumi ya gana da shugaban ƴanbindigar Dogo Gide tare da wasu manyan shugabannin ƴanbindigar a dajin Dutsen Magaji.

Majiyar DCL Hausa ta shaida cewa gwamnatin jihar Neja ta aike da wakilanta don tattaunawa da ƴanbindigar domin kubutar da daliban.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply