Home Addini Ana gudanar da shagulgulan karamar salla a Jamhuriyar Nijar

Ana gudanar da shagulgulan karamar salla a Jamhuriyar Nijar

205
0

A wannan asabar ce al’ummar musulmin Jamhuriyar Nijar ke gudanar da bikin karamar salla bayan sanarwar ganin jinjirin watan a ranar Juma’a a wasu sassan wanda ya kawo karshen watan azumin Ramadan.

Da misalin karfe 9 ne dai na safe kamar yadda aka saba babban limamin jahar Damagaram na babban ya jagoranci salla rakka’a biyu kamar yadda addinin musulumci ya tanadar.

Sallar Idi a Nijar

Bayan kammala sallar babban limamin ya gudanar da huduba a harshen larabci kafin daga bisani gwamnan jahar Damagaram da mai martaba sarkin Damagaram suka yi wani takaitaccen jawabin barka da salla ga al’ummar jahar.

A yanzu haka dai ana nan ana ci gaba da gudanar da shagulgulan sallar duk da yanayin da ake ci na wannan annoba ta coronavirus.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply