Home Kasashen Ketare Ana gudanar da zaben kananan hukumomi a Nijar

Ana gudanar da zaben kananan hukumomi a Nijar

113
0

Tun da misalin karfe 8 na safiyar Lahadin nan ne aka bude rumfunan zabe na matakin kananan hukumomi a fadin kasar jamhuriyar Nijar.

Ya zuwa yanzu, zaben dai na wakana ba tare da wasu matsaloli ba, ko da ya ke rahotanni daga wasu sassan jihohin Damagaram da Tahoua na cewa an samu jinkirin kai kayen zaben.

Sama da mutane miliyan 7 ne dai ake sa ran za su kada kuri’arsu domin zaben kansiloli na matakin shiyyoyi, da na da’irar birane da ma na jiha.

Wannan zabe dai na zama kamar na sharar fage ga na ‘yan majalisar dokoki da na shugaban kasa da za a yi su nan da makonni biyu masu zuwa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply