Home Labarai Ana korar malamai silar IPPIS – ASUU

Ana korar malamai silar IPPIS – ASUU

69
0

Ƙungiyar malaman jami’o’in Nijeriya ASUU, ta ce ƙoƙarin gwamnatin tarayya na saka malaman jami’o’in a tsarin tattara bayanai na IPPIS, ya yi silar korar malaman wucin gadi a jami’o’in.

ASUU ta bada misali da jami’ar Bayero da ke Kano, da jami’ar tarayya da ke Wukari jihar Taraba, inda aka kori malaman wucin gadin.

Wanda ta ce hakan ya saɓawa ƴan jami’o’i na ɗaukar malaman da suka da ce, kamar yadda ya ke faruwa a faɗin duniya.

Shugaban na ASUU Farfesa Biodun Ogunyemi ya bayyana haka a zantawar sa da ƴan jarida, ya ce har yanzu malaman jami’o’in Maiduguri da Michael Okpara ba su samu albashin su na watan Fubrairu ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply