Home Labarai Ana satar wa mata Panties (bante) a wasu jihohin Nijeriya

Ana satar wa mata Panties (bante) a wasu jihohin Nijeriya

67
0

[cmsmasters_row data_shortcode_id=”2gqpjt21fc” data_padding_bottom_mobile_v=”0″ data_padding_top_mobile_v=”0″ data_padding_bottom_mobile_h=”0″ data_padding_top_mobile_h=”0″ data_padding_bottom_tablet=”0″ data_padding_top_tablet=”0″ data_padding_bottom_laptop=”0″ data_padding_top_laptop=”0″ data_padding_bottom_large=”0″ data_padding_top_large=”0″ data_padding_bottom=”50″ data_padding_top=”0″ data_bg_parallax_ratio=”0.5″ data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center” data_color=”default” data_bot_style=”default” data_top_style=”default” data_padding_right=”3″ data_padding_left=”3″ data_width=”boxed”][cmsmasters_column data_width=”1/1″ data_shortcode_id=”w0y6bkps4k” data_animation_delay=”0″ data_border_style=”default” data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center”][cmsmasters_text shortcode_id=”dxgnc8vjse” animation_delay=”0″]

Ana ci gaba da samun barayin Panties (bante) na mata a jihar Legas da ke kudancin Nijeriya, acewar gidan rediyon Deutsche Welle kamar yadda ya bayar da rahoto a cikin shirinsa na safiyar Juma’a 27.09.2019.

Barayi dai yanzu a Legas na rungumar wannan dabi’a ta satar Pantis din mata domin samun kudi. Pantis dai shi ne abu na karshe da barawo zai iya sata idan ya je sata a gidajen mutane. Sai dai kuma a yanzu ana samun barayin da babu abin da suke so su sata in ba Pantis din ba.

Juliet wata matashiya ta shaida wa DW cewa “na dade ina jin ana sace pantis din mata, da ban yarda ba sai da aka sace nawa bayan da na shanya su tagar dakina. Barawon ya fasa tagar ya sace su. Ina ganin haka na ruga coci domin neman tsari daga makiricin da aka iya biyo baya”

Jama’a a Kudancin Nijeriya dai na alaqanta satar Pantis da yawaitar matsafa wadanda ke bukatar akai musu tsofaffin Pantis din da mata ke amfani da su don yin surkulle.

Wata matshiya da aka sace mata Pantis din ta ce ” Bayan dana gano an sace pantis dina na shiga damuwa ko bacci ma na kasa yi saboda suna karbe min sa’a ko kuma toshe min mahaifata. Ina adduar Allah Ya sa su manta da pantis a wani wuri kafin su kai ga inda suke son zuwa”

Rundunar yan sanda ta jihar Legas a tabakin mai magana da yawunta Bala Elkana ta tabbatar da bullar wannan dabi’a. Ya kuma ce sun ma taba kama wasu mutum biyu da suka saci pantis suka sayar amma rikici ya kaure a tsakaninsu bayan da suka zo rabon kudi.

Ba jihar Legas ce kadai ke fama da wannan dabi’a ba, wata daliba a kwalejin ilimi ta tarayya da ke Zaria ta tabbatar wa da jaridar DCL Hausa cewa a yanzu haka ‘yan mata na kaffa-kaffa da pantis din su don gudun kada a sace su.

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply