Home Labarai “Ana shirin yin aure tsakanin dan jihar Katsina da wata ‘yar kasar...

“Ana shirin yin aure tsakanin dan jihar Katsina da wata ‘yar kasar Rasha”

83
1

Wani hoto da safiyar ranar Talatar nan na ci gaba da yaduwa a shafukan sada zumunta dauke da hotan wani matashi da aka ce dan jihar Katsina ne tare da wata da aka ce ‘yar kasar Rasha ce kuma suna shirin yin aure.

Wani mai suna Iyal Sambo ya rubuta a shafinsa na facebook cewa “This Katsina guy got his own from Russia, am very sorry for NIGERIAN slay QUEENS!” wato ke nan yana sanar da jama’a cewa ga wani matashi dan jihar Katsina shi ma ya samu mata daga kasar Rasha, a don haka ‘yan matan Nijeriya sai su kara daura damara”.

 

Hotan matashin Katsina da aka ce zai auri ‘yar kasar Rasha

Jaridar Katsina Post ce ta fara wallafa wannan labari. Sai dai ta ce kawo yanzu ta gaza tabbatar da sahihancin wannan hoto da kuma samun karin bayani a kan wannan yunkuri. Har ila yau DCL Hausa ita ma ba ta kai ga tabbtar da sahihancin labarin ba, amma da alama wannan labari yana samun karbuwa a saboda yadda a kwanannan wani matashi a jihar Kano ya samu wata mata daga kasar Amirka wace ta  bukaci a daura musu aure su tafi Amirka da matashin don bude sabuwar rayuwa duk da cewa matashin yana da shekaru 23 yayinda ita kuma take da shekaru 45.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

1 COMMENT

  1. Allah ya kyauta yasa sanadin shigarta musulunci kenan saidai yanzu naga samari sundage wajen friending din turawa saboda kwadayi suma kuma ba kudi kukaji ance sunbasu ba

Leave a Reply