Home Kasashen Ketare Mai haƙar kabari ya ƙwalƙwale haƙoran zinarin gawa

Mai haƙar kabari ya ƙwalƙwale haƙoran zinarin gawa

234
0

‘Ƴansanda a jihar Bavaria da ke Tarayyar Jamus sun kai samame a gidan wani ma’aikacin maƙabarta tare da samun haƙoran zinari 11 da zobe guda a wajensa.

Mutumin wanda ake tuhuma da takurawa matattu, ana zargin ya ƙwalƙwalo zinarin ne daga gawarwakin da aka rufe a babbar maƙabartar birnin Wurzburg, kamar yadda Sashen Turanci na Deutsche Welle ya bayar da labari.

Wata sanarwa da ƴansandan suka fitar, sun ce mutumin da ake tuhuma da hana matattu zama lafiya, ya cire zinarai a jikin gawarwaki aƙalla sau 20 tun daga shekarar 2019.

‘Ƴansandan sun kai samame gidan mutumin ne bayan sun samu bayanan sirri, inda kuma suka samu zinari mai nauyin gram 30.

Sai dai wand ake zargin ya shaida wa ‘yan sanda cewa ya dauko zinaren daga jikin gawarwakin domin ya nuna wa abokanansa ba wai domin ya sata ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply