Home Labarai Ana zargin miji da shan jinin al’adar matarsa a Kano

Ana zargin miji da shan jinin al’adar matarsa a Kano

191
0

Kotun shari’ar musulunci ta daya karkashin jagorancin Mai shari’a Abdullahi Halliru Kofar Na’isa ta fara sauraron karar da wata mata ta shigar a gabanta tana rokon kotu ta raba aurensu da mijinta.

Matar ta bayyana wa kotu cewa mijinta na yi mata surkulle, har ta ga yi mata barazana da wuka kan cewa lallai sai ta bashi dama ya sha jinin al’adarta domin biyan bukatarsa.

Freedom Radio ta rawaito cewa mijin yace atafau wannan magana babu ita, kalar sharri ne kawai.

Kotu ta saka ranar 24 ga watan gobe Disamba din cigaba da sauraron karar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply