Home Labarai Ana zargin tsohon minista da cin amanar kasa saboda shiga fadar shugaban...

Ana zargin tsohon minista da cin amanar kasa saboda shiga fadar shugaban kasa da bindiga

82
0

An gurfanar da wani tsohon ministan Saliyo a gaban kotu bisa zargin cin amanar kasa, bayan ya shiga fadar shugaban kasa da bindiga.

An dai gurfanar da tsohon ministan Tsaron kasar Paolo Conteh a wata kotu da ke Freetown kan zarge-zarge 16 da ke da alaka da cin amanar kasa.

A zaman kotun ne aka karanto masa zarge-zargen da ake yi masa tare da dage sauraron karar ba tare da an bashi beli ba.

A ranar 19 ga watan Maris ne dai aka kama Mista Conteh, saidai ya ce tun da farko ya shaidawa jami’an tsaron fadar shugaban kasar cewa yana dauke da bindiga, amma dai hukumomin kasar sun ce gano ta aka yi a jikin sa.

Tsohon ministan ya je fadar shugaban kasar ne don gudanar da wani taro kan coronavirus.

Kafafen yada labarun kasar dai sun ruwaito cewa, kundin tsarin mulkin kasar ya ayyana cewa shiga taro da shugaban kasa dauke da makami ko bindiga, cin amanar kasa ne.

Zuwa lokacin hada wannan labari dai, kasar ta Saliyo bat a da rahoton bullar cutar ta coronavirus.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply