Home Kasashen Ketare Juyin Mulki A Sudan: Anso ayi kare jini biri jini a Sudan

Juyin Mulki A Sudan: Anso ayi kare jini biri jini a Sudan

108
0

Juyin Mulki A Sudan: AN SO AYI KARE-JINI-BIRI-JINI A SUDAN.

Hankulan jama’ar Sudan sun fara kwanciya bayan da a jiya wasu daga cikin sojojin kasar suka yi yunkurin kifar da Gwamnatin Soji dake mulki a kasar.

Janaral Jamal Omar ya ce sojoji masu biyayya ga gwamnatin soji sun yi nasarar dakatar da yunkurin juyin mulkin da aka so a yi musu.

A cikin jawabi na musamman da ya yi a gidan talabijin na kasar, Janar din yace kawo yanzu sun kama manyan sojoji guda 12 da kananan sojoji guda 4 da ake zargin sun kitsa wannan juyin mulkin.

Sudan dai ta kasa samun zaman lumana tun bayan da masu zanga zanga suka fara yi wa tsohon Shugaba Albashir bore akan janye tallafi akan burodi, zanga zangar da a karshe ta kifar da gwamantin Shugaba Umar Albashir.

Shin akwai darasi da kasashen Afrika za su iya koya daga abinda ke faruwa a Sudan?

#ZuD

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply