Home Kasashen Ketare Anyi fito-na-fito tsakanin fararan hula da jami’an tsaron Nijar

Anyi fito-na-fito tsakanin fararan hula da jami’an tsaron Nijar

66
0

Al’ummar babban birnin Yamai karkashin jagorancin gamayyar kungiyoyin fararan hula ne suka fito kan titunan birnin dan gudanar da zanga-zangar nuna goyan baya ga jami’an tsaron kasar, wadanda a baya bayan ‘yan ta’adda ke kai musu hari.

Bayan kammala sallar Juma’a ne dai dandazon al’ummar ta fito dan amsa kiran jagororin kungiyoyin fararan hula da suka dade suna yi ga al’umma.

To sai dai a na ta wajen, gwamnatin kasar tun da sanyin safiyar ranar Juma’a din nan ta jibge jami’an tsaron kan dukkan wasu muhimman titinan birnin Yamai dan hana gudanar da wannan zanga-zanga duk da yake daman ta ki amincewa da takardar bukatar yin zanga-zanga da kungiyoyin suka nemi.

Wannan mataki ne ma ya kara bakanta ran al’ummar da suka fito inda suka nemi huce fishinsu kan kone-konan taya da jifar jami’an tsaron sai dai suma sun mayar da martani ta hanyar jefa hayaki mai sa hawaye.

Daman dai kungiyoyin farar hular sun sha ajjiye takardar neman izinin zanga-zangar lumanar, gwamnatin kuma tana kin amincewa da bukatar tasu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply