Jam’iyyar APC a jihar Kebbi ta janye dakatarwar da ta yi wa shugabanta na jihar, Hon. Abubakar Kana Zuru, tare da mayar da shi kan mukaminsa bayan tuntubar shugabannin jam’iyyar daga matakin yanki zuwa jiha.
Jami’in hulda da jama’a na APC a jihar Kebbi, Isah Assalafi, ne ya tabbatar da matakin a wata hira da DCL Hausa, inda ya ce an cimma matsayar ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.
Ya bayyana cewa tun farko an dakatar da Kana Zuru ne bisa zargin daukar wasu matakai da suka shafi harkokin jam’iyyar ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki ba, musamman wajen gudanar da wasu ayyukan jam’iyyar.
Da aka tambaye shi ko matsin lamba ne ya sa aka dawo da shugaban kan mukaminsa, Assalafi ya musanta hakan, yana mai cewa matakin ya biyo bayan shawarwari da tuntubar juna tsakanin shugabannin jam’iyyar.
Jami’in ya shawarci Kana Zuru da ya rika tafiya da kowa tare da yin la’akari da darussan da aka koya daga abubuwan da suka faru a baya, domin kauce wa sake samun irin wannan matsala.
Ya ce dakatarwar ta samo asali ne daga abubuwan da suka faru yayin zaben da aka gudanar a karamar hukumar Zuru ta jihar Kebbi.
Game da rade-radin cewa dakatarwar ta haddasa baraka a jam’iyyar, ya ce irin wannan mataki na iya bata wa wasu magoya baya rai, amma ya tabbatar da cewa yanzu an shawo kan lamarin.
A cewar Assalafi, an fara yanke shawarar dakatar da shugaban tun ranar 20 ga Yuni, 2026, amma bayan shawarwari da tuntubar masu ruwa da tsaki, a ranar 1 ga Oktoba, 2026, jam’iyyar ta ga ya dace ta janye matakin tare da mayar da Abubakar Kana Zuru kan mukaminsa.
