Home Sabon Labari APC: an dakatar da mataimakin gwamnan jihar Kogi

APC: an dakatar da mataimakin gwamnan jihar Kogi

77
0

Daga Abdullahi Garba Jani

 

Jam’iyyar APxC ata dakatar da mataiamakin gwamnan jihar Kogi Mr Simon Achuba bisa zargin cin amanar jam’iyya.

Da ya ke zantawa da manema Labarai da yammacin Alhamis a birnin Lokoja, shugaban Jam’iyyar APC na jihar Abdullahi Bello, ya ce an samu mataimakin gwamnan jihar dumu-dumu da aikata zambo-cikin-aminci ga Jam’iyyar kafin da bayan babban zaben 2019.

Jaridar Daily Nigerian ta ba da rahoton cewa akwai zaman doya da manja tsakanin gwamnan jihar Yahaya Bello da mataimakinsa Mr Simon Achuba bisa zargin bambancin ra’ayi na siyasa.

A ranar Larabar makon nan majalisar dokokin jihar ta yi yunkurin tsige mataimakin gwamnan bisa zargin badakalar kudi da sauran wasu ayyukan da ba su dace ba.

Akwai ma zarge-zargen da mataimakin gwamnan ke yi na cewa gwamnan jihar Yahaya Bello na barazana ga rayuwarsa. Sannan shi kuma ya yi barazanar maka gwamnan kotu kan cewa ya rike masa albashi da sauran wasu hakkokinsa tun daga 2017 har zuwa yanzu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply