Home Labarai APC nada kwarin guiwar lashe zaben gwamnan Ondo – Osita

APC nada kwarin guiwar lashe zaben gwamnan Ondo – Osita

168
0

Wani mamba a kwamitin da jam’iyyar APC ta kafa kan zaben gwamnan jihar Ondo, Mista Osita Okechukwu, ya yi watsi da fargabar cewa jam’iyyar APC mai mulki na iya shan kaye.

Okechukwu, ya bayyana hakan ne yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja.

Ya ce ba shi da wata fargaba saboda akwai bambanci sosai tsakanin Gwamna Rotimi Akeredolu da takwaransa na Jihar Edo, Godwin Obaseki.

“Don haka jam’iyyar APC ce ke da nasara a zaben da za a gudanar a ranar 14 ga watan gobe” inji shi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply