Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta lashe dukkanin kujeru 44 na shugabannin kananan hukumomi da ma kujeru kansiloli guda 484 na jihar, a zaben kananan hukumomin da aka gudanar ranar Asabar.
Ibrahim Garba-Sheka, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na jihar ne ya bayyana hakan yayin sanar da sakamakon zaben a ranar Lahadi a Kano.
Garba-Sheka ya ce an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali a gabadaya rumfunan zabe guda 11,500 da ke fadin jihar.
