Home Sabon Labari Arsenal ta ɗauko Willian daga Chelsea

Arsenal ta ɗauko Willian daga Chelsea

122
0

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta ƙulla yarjejeniya da ɗan wasan Brazil Willian mai buga wasa a ƙungiyar Chelsea.

Ɗan wasan mai shekaru 32 ya amince da yarjejeniyar shekaru uku a Arsenal bayan kwantiraginsa a Stamford Bridge ya ƙare a ƙarshen kakar wasan da aka kammala ta 2019/20.

Willian ya shafe kakar wasanni 7 a Chelsea inda ya taimaka mata lashe kofin firimiya guda 2, sannan ya buga wasannin firimiya 234 a tsohuwar kungiyar6 ta shi, inda ya ci ƙwallaye 37 da kuma taimaka aci kwallaye6 33 a duk wasannin 234 na firimiya da ya buga a Chelsea.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply