Mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta, ya yi alwashin kungiyarsa na da damar taka rawar gani fiye da yadda ta yi a kakar wasan da ta gabata, bayan da ta ci gaba da samun cikakken maki a gasar Premier League ta bana.
Jaridar Punch ta ruwaito yadda Arsenal ta samu nasarar doke Chelsea da ci 2-1 a filin wasa na Emirates ranar Lahadi, bayan da Morgan Rogers ya fara jefa wa Chelsea kwallo, yayin da Kai Havertz da Martin Ødegaard suka ci wa Arsenal kwallayen da suka sauya sakamakon wasan.
Arteta ya bayyana wasan da Arsenal ta yi a matsayin na musamman, yana mai cewa nasarar da suka samu a kan Chelsea ta nuna irin damar da kungiyar ke da ita a wannan kakar.
Ya ce komai zai dogara ne kan yadda ‘yan wasansa za su ci gaba da nuna kishin aiki, juriya da kuma kokarin inganta kansu.
Kocin ya kuma yaba wa kyaftin din kungiyar, Martin Ødegaard, inda ya ce dan wasan na cikin yanayi mafi kyau da ya taba ganinsa a Arsenal.
Arteta ya danganta hakan da samun cikakkiyar lafiyar jiki, karuwar kwarin gwiwa da kuma yadda yake jin dadin buga kwallon kafa.
A cewar Arteta, Ødegaard ya taka muhimmiyar rawa a wasansu da Chelsea, inda ya rika kai hari, yin kokarin zura kwallo da kuma samar da damar cin kwallo ga abokan wasansa.
Ya ce hadin gwiwar da Ødegaard ke samu da sauran ‘yan wasan Arsenal na taimaka masa wajen kara nuna kwarewarsa.
Arteta ya kuma yi tsokaci kan Kai Havertz, inda ya bayyana cewa dan wasan na Jamus yana cikin farin ciki kuma ya samu kwanciyar hankali a kungiyar.
Ya ce Havertz ba wai kawai yana zura kwallaye ba ne, har ma bayar da gagarumar gudummawa wajen taimaka wa kungiyar a sauran bangarorin wasa.
Kocin na Arsenal ya jaddada cewa har yanzu kungiyarsa na da damar kara inganta wasanta, yana mai cewa burinsu shi ne kowanne dan wasa da kuma kungiyar baki daya su ci gaba da samun sabon matsayi na kwarewa.
Ya jaddada cewa idan ‘yan wasa suka kara inganta, kungiyar ma za ta kara karfi, kuma hakan shi ne babban burinsu a kakar bana.
