Home Addini Ashura: Ana kai-ruwa-rana tsakanin ‘yan shi’a da jami’an tsaro a...

Ashura: Ana kai-ruwa-rana tsakanin ‘yan shi’a da jami’an tsaro a Katsina

80
0

[cmsmasters_row][cmsmasters_column data_width=”1/1″][cmsmasters_text]

Mabiya mazhabar Shi’a a Nijeriya sun zargi cewa jami’an
tsaro na farautar rayuwarsu a Katsina, mahaifar shugaba Buhari.

A wata hira da jaridar DCL Hausa ta yi da Zainab Lawal
Abdulkadeer  wata matashiya mai bin
wannan mazhaba ta ce sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun yi harbi
akan jama’arsu da suka fito a garin Katsina, zargin da wannan jarida ba ta iya
tabbatar wa a wannan lokaci.

Da jaridar DCL Hausa ta tambaye ta me ya sa suka fito
muzaharar Ashura bayan jami’an tsaro tun kafin yau sun gargade su akan kar su
fito? Sai ta ce ” Mu bayin Allah ne kuma kasa ta Allah ce kuma addinin
Allah muke yi, su yi nasu mu yi namu mana ! Babu wanda ya isa ya hana mu bautar
Allah, kar mu fito bisa wannan dalili? Mu muna jimamin kisan da aka yi wa Imam
Hussaini jikan Manzon Allah (S.A.W) ne”

Zainab Lawal Abdulkadeer wata matashiya mai bin mazhabar shi’a a Katsina

Ta ci gaba da cewa su ‘yan shi’a sun gane cewa gwamnati na
yunkurin ganin ta karar da su gaba daya. Da wakilinmu ya ce ma ta, DCL Hausa ba
ta  da hujjar yarda da wannan zargi sai
ta ce ” Wannan magana tabbatacciya ce, idan ba haka ba me nene dalilin da
ya sa kullum gwamnatin Nijeriya kashe mu take”.

Mabiya mazhabar Shi’a dai sun sha nanata cewa su ba ‘yan
ta’adda bane duk da cewa a watannin baya gwamnatin Nijeriya ta samu izinin kotu
na ta kira su da sunan ‘yan ta’adda.

Sai dai ‘yan shi’a na ci gaba da musanta wannan zargi. Amma
duk da cewa ba a ganinsu da bindigogi jam’a na ganinsu a wasu lokutta a baya
suna fareti irin na soja

Saurari sautin hirar DCL Hausa da Zainab mai bin mazahabar
shi’a

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply