Home Labarai Atiku ya ƙaryata karɓar rigakafin Covid-19

Atiku ya ƙaryata karɓar rigakafin Covid-19

136
0

Ƙungiyar Atiku Support Organisation ASO, ta ƙaryata rahoton da ke cewa an yi wa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar allurar rigakafin Covid-19 na kamfanin Pfizer, a ƙasar Haɗadɗiyar Daular Larabawa.

Wani daga cikin ƴan tawagar yaɗa labaran Atiku ne dai, Abdulrasheed Uba Sharaɗa ya wallafa wasu hotuna a shafinsa na Twitter a ranar Talata, dake nuna lokacin da ake yi wa Atiku allurar.

Saidai kuma mataimakin Daraktan ƙungiyar ta ASO na ɓangaren soshiyal midiya Muhammad Sanusi Hassan ya ƙaryata labarin, yana mai cewa an ɗauki hotunan ne a wani asibiti amma ba wurin rigakafin cutar ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply