Ɗan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce zai kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a ƙasar cikin shekara guda da hawansa mulki, idan aka zaɓe shi a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Tun bayan fara harkokin siyasa gabanin zaɓen 2027, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ci gaba da jan hankalin jama’a da wasu manufofinsa, ciki har da sabon alkawarinsa na dawo da tallafin man fetur, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce daga gwamnati da wasu ’yan Nijeriya.
Atiku ya bayyana matsayinsa ne a wata hira da BBC Hausa, inda ya ce gwamnatinsa za ta ɗauki matakan da suka dace domin magance matsalar tsaro cikin shekara ɗaya.
Ya ce za a ƙara yawan jami’an tsaro tare da samar musu da kayan aiki da isasshen kuɗaɗen gudanar da ayyukansu.
Ya kuma ce zai tallafa wa matasa wajen kafa sana’o’i, domin a cewarsa rashin aikin yi na daga cikin abubuwan da ke jefa wasu matasa cikin aikata laifuka.
Atiku ya ƙara da cewa zai tattauna da shugabannin ECOWAS domin farfaɗo da rundunar ECOMOG, tare da ƙarfafa haɗin gwiwar sojojin ƙasashen yankin wajen yaƙi da matsalar tsaro.
A cewarsa, Nijeriya za ta iya haɗa ƙarfi da ƙasashen Côte d’Ivoire, Sierra Leone da Liberia domin ƙara tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Dangane da Nijeriya da Nijar, Atiku ya ce juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar bai kamata ya zama dalilin da zai sa Nijeriya ta katse dangantakarta da ƙasar ba.
Ya ce ƙasashen biyu na da dadaddiyar alaƙa kuma al’ummominsu na da kusanci.
Ya kuma bayyana aniyarsa ta yin aiki domin dawo da Nijar, Burkina Faso da Mali cikin ƙungiyar ECOWAS, yana mai cewa haɗin kan ƙasashen zai taimaka wajen rage rashin aikin yi da kuma matsalolin tsaro.
Game da zaɓen 2027, Atiku ya nuna shakku kan ikon INEC na gudanar da sahihin zaɓe, amma ya buƙaci ’yan Nijeriya su fito ƙwarai su kaɗa ƙuri’a tare da kare ƙuri’unsu domin tabbatar da cewa wanda suka zaɓa shi ne wanda za a bayyana a matsayin wanda ya yi nasara.
Atiku ya kuma ce zaɓen 2027 zai kasance ƙoƙarinsa na ƙarshe na neman shugabancin Nijeriya.
Ya ce idan bai samu nasara ba, zai ci gaba da ba matasan ’yan siyasa shawarwari idan suka nemi taimakonsa.
A kan batun dawo da tallafin man fetur, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce bai kamata a cire tallafin gaba ɗaya cikin lokaci ɗaya ba.
Ya ce idan ya zama shugaban ƙasa, gwamnatinsa za ta tantance halin da ake ciki tare da tuntuɓar masu ruwa da tsaki kafin yanke hukunci.
Atiku ya ce irin wahalhalun da ’yan Nijeriya ke fuskanta a yanzu sun fi duk wata wahala da ya taɓa gani a cikin shekaru 79 na rayuwarsa.
Ya kuma zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da cire tallafin mai gaba ɗaya, yana mai cewa matakin ya jefa jama’a cikin tsananin wahala har ya shafi harkokin noma da kasuwancinsa.
