Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya taya murna ga Mr Joe Biden bayan lashe zaben shugabancin Amurka da ya yi.
Atiku Abubakar a shafinsa na Facebook ya wallafa cewa ba wai murna kadai ya ke taya Biden ba, har ma yana kira gare shi da ya kara inganta alakar da ke tsakanin Amurka da Nijeriya.
Ya ce lallai Amurkawa sun yi kyakkyawan zabi, ganin yadda suka zabi wanda zai shiga gaba a kawo karshen ta’addanci da sauran matsalolin tsaro.
