Home Labarai Aure: mata ta maka mijinta kotu don ba ya son ‘ya’ya da...

Aure: mata ta maka mijinta kotu don ba ya son ‘ya’ya da yawa

84
0

Abdullahi Garba Jani

Wata matar aure mai shekaru 27 mai suna Fa’iza Yusuf ta maka mijinta mai suna Muhammad Abubakar a gaban kotun shari’a da ke zamanta a Rigasa, Kaduna take neman mijinta ya saketa sabo da ba ya son yawan haihuwar ‘ya’ya.

Fa’iza Yusuf da ke zaune a Unguwar Nasarawa, Kaduna ta fada wa kotu cewa mijinta ba ya so ta haifar ma sa ‘ya’ya.

“Yanzu muna da ‘ya’ya, amma dai ba ya son kari a kan hakan. Ya ma yi barazanar cewa ba cikinsa bane muddin ya ganni da ciki” ta yi zargi.

Wanda ake kara dai bai samu halartar zaman kotun ba duk kuwa da cewa an kai ma sa sammaci.

Alkalin kotun Malam Dahiru Bamalli ya umurci mai karar da ta gabatar da iyayenta a ranar 30 ga watan Disamba mai zuwa.

Kotunan jihar Kaduna dai na yawan samun kararraki masu alaka da zaman aure. Ko ‘yan makonnin da suka gabata sai da wata kotu ta saurari karar wata mata da ta kai karar mijinta bisa zargin ba ya sallah.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply