Home Labarai Auren Dole: Budurwa ta kashe kanta a Gombe

Auren Dole: Budurwa ta kashe kanta a Gombe

232
0

Wata budurwa ‘yar asalin jihar Gombe mai suna Amina Isah ta kashe kanta sakamakon auren dole da iyayenta suka yi mata.

Kamar yadda jaridar “Muryar ‘Yanci” ya tattauna da Wata kawarta, ta bayyana cewa, ita Amina tana soyayya ne da wani wanda take so mai suna Muhammad, daga bisani kuma iyayenta suka tilasta mata auren wani wanda ba ta so, hakan ya kai ga iyayenta sun aura mata wanda suke so alhali kuma ita ba ta son shi.

Kafin dai budurwar ta sha madarar fiya-fiya ta mutu ta yi wa wasu daga cikin kawayenta
sakon text, wadanda suka hada da Hassana, Zahra, Da Aisha, akan cewa ita fa muddin aka mata auren dole to ba makawa za ta kashe kanta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply