Home Labarai Ayyukan Gwamnati: Majalisar Wakilai za ta bi diddigin ayyukan da aka yi...

Ayyukan Gwamnati: Majalisar Wakilai za ta bi diddigin ayyukan da aka yi watsi da su

129
0

Daga: Nuruddeen Ishaq Banye

 

Majalisar Wakilai ta tarayyar Nijeriya za ta bi diddiƙin dukkan wasu ayyukan da aka yi watsi da su, wadanda gwamnatin tarayya ta bada kwangila daga shekarar 1999 zuwa yau, ba a kammala ba.

Matakin majalisar ya biyo bayan wani ƙudiri mai taken binciken ayyukan da ba a kammala ba, wanda Mista Francis Uduyok ya gabatar a zaman majalisar na ranar Laraba.

Shugaban Majalisar Wakilan Nijeriya

Majalisar ta ce akwai ayyuka sama da dubu ashirin (20,000) da suka kai darajar biliyoyin nairori da aka watsar ba a kammala ba duk da cewa gwamnatin ta biya sama da kashi 50 cikin dari na kuɗin ayyukan.

Dama dai ko a karshen makon jiya, hukumar yaƙi da cin hanci ta ICPC ta yi bayanin cewa sama da Naira Tiriliyan biyu aka kashe wajen ayyukan mazaɓu a tsakanin wannan lokaci, ba tare da kwalliya ta biyu kuɗin sabulu ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply