Home Coronavirus Ba a samu sabbin kamuwa da Covid-19 ba a Nijar

Ba a samu sabbin kamuwa da Covid-19 ba a Nijar

122
0

Sakamakon gwajin cutar Covid-19 na ranar Alhamis a Jamhuriyar Nijar da ma’aikatar kiwon lafiya ta fitar ya nuna cewa ba’a samu ko mutum ɗaya da ya ƙara kamuwa da cutar a faɗin ƙasar ba.

A baya-bayan nan dai ƙarfin yaɗuwar cutar na ƙara raguwa, lamarin da ya sa hukumomin ƙasar ke ɗaukar matakan sassauta wasu dokokin da aka saka lokacin da cutar ta ɓulla a ƙasar.

A yanzu haka dai mutum 88 ne suka rage masu ɗauke da cutar a fadin Nijar yayin da 803 suka warke sai kuma 64 da suka rigamu gidan gaskiya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply