Home Labarai Ba a yi wa Fulani adalci a Nijeriya – Isah Yuguda

Ba a yi wa Fulani adalci a Nijeriya – Isah Yuguda

25
0

Tsohon gwamnan jihar Bauchi Malam Isah Yuguda, ya nuna ɓacin ransa kan yadda ake alaƙanta Fulani makiyaya da ƴanta’adda.

Da yake fira da ƴanjarida ranar Litinin, bayan sabunta rajistarsa ta APC a Bauchi, Yuguda ya ce ko kusa ba a yi wa Fulani adalci a Nijeriya.

Ya ce gwamnatin tarayya ta yi ko oho da Fulani, waɗanda ke samar da shanu sama da miliyan ɗaya da ake yanka wa a kullum cikin ƙasar.

A cewarsa, idan har gwamnati za ta iya ware maƙudan kuɗi wajen tallafawa manoma, babu dalilin da za a ƙi ware irin waɗannan kuɗi a tallafi makiyaya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply