Home Lafiya Ba batun hana zirga-zirga a fadin Nijeriya – PTF

Ba batun hana zirga-zirga a fadin Nijeriya – PTF

122
0

Shugaban kwamitin shugaban ƙasa na yaƙi da cutar coronavirus Dr Sani Aliyu, ya ƙaryata batun shirin hana yawo a faɗin Nijeriya don hana yaɗuwar cutar.

Shugaba Buhari dai ya sanar da rufe jihohin Lagos, Ogun da Abuja, na tsawon makonni biyu kafin daga bisani a ƙara wasu makonnin biyu.

Saidai a lokacin taron yin jawabi kan halin da ake ciki a kan cutar karo na 17 da ya gudana jiya Laraba a Abuja, Aliyu ya nisanta kan sa ga labarin da ake yaɗawa na rufe ƙasar.

Ya nanata cewa kwamitin nasa bai fitar da wata sanarwa kan ɗaukar matakin rufe ƙasar ba.

Shugaban kwamitin ya gargaɗi kafafen yaɗa labarai da sauran al’umma kan irin labaran da za su riƙa yaɗawa.

Ya ce duk wani bayani da za a fitar kan matakan gaggawa da ake ɗauka ana sanar da su ne kaɗai a lokacin irin wannan taro ba wai wata hanya daban ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply