Wasu al’ummar jihar Yobe da masu rajin kare haƙƙin jama’a sun soki gwamna Mai Mala Buni kan alkawarin bayar da Naira miliyan 300 ga ƙungiyar jama’atu izalatil bid’ah wa iqamatis sunnah, JIBWIS, domin tallafa wa shirin gina jami’ar Musulunci.
Sai dai gwamnatin jihar ta bayyana cewa kuɗin gudummawar na gwamnan ne da kansa, ba daga asusun gwamnatin Yobe aka bayar da su ba.
Jaridar Punch ta ruwaito Gwamna Buni ya bayyana alkawarin bayar da kuɗin ne a birnin Jos na jihar Plateau, yayin wani taron ƙasa da JIBWIS ta shirya kan bunƙasa shiga harkokin siyasa da tabbatar da adalci a zamantakewa domin ƙarfafa haɗin kan Nijeriya da ci gabanta.
Sai dai wasu mazauna jihar da masu fafutuka sun ce akwai buƙatar gwamnatin ta fi mayar da hankali kan matsalolin ilimi, kiwon lafiya da sauran muhimman ayyukan more rayuwa. Yayin da wasu suka nuna damuwa kan yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma lalacewar wasu makarantun gwamnati, yayin da wasu suka ce ana bukatar ƙarin kayan aikin jinya, musamman cibiyoyin kula da masu fama da cututtukan koda.
Daya daga cikin masu fafutuka, Adamu Bello Jana, ya shaida wa jaridar Punch yadda fannin ilimi ke zaman ɗaya daga cikin bangarorin da ke bukatar kulawar gaggawa a Yobe, yana mai cewa Naira miliyan 300 za su iya taimakawa wajen gyara wasu daga cikin matsalolin da makarantun jihar ke fuskanta.
Sai dai a martaninsa, darakta janar na yaɗa labarai da harkokin kafafen yaɗa labarai ga gwamnan Yobe, Mamman Mohammed, ya ce rahotannin da ke nuna cewa an yi alkawarin bayar da kuɗin ne a madadin gwamnatin jihar ba su da tushe.
A cewarsa, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa, Kabiru Masari, ya sanar da gudummawar naira miliyan 300 da ya bayar da kansa, tare da wani alkawarin naira miliyan 300 da ya bayar a madadin gwamna Buni domin gina jami’ar JIBWIS.
Mohammed ya jaddada cewa gudummawar da aka bayar a madadin gwamna Buni tasa ce ta kashin kansa, ba ta gwamnatin jihar Yobe ba, yana mai cewa Kabiru Masari ba shi da ikon yanke hukunci ko yin alkawarin kuɗi a madadin gwamnatin jihar.
Ya bayyana zargin cewa za a biya kuɗin daga asusun gwamnatin Yobe a matsayin ƙarya, kuskure da kuma kokarin karkatar da gaskiya. Duk da wannan bayani, muhawarar da ta biyo bayan tallafin na ci gaba da mayar da hankali kan yadda ya kamata a tsara fifikon kashe kuɗi tsakanin ayyukan addini da kuma buƙatun ilimi, kiwon lafiya da sauran muhimman ayyukan jama’a a jihar Yobe.
