Home Coronavirus Ba da son ranmu aka buɗe makarantu ba – Gwamnatin tarayya

Ba da son ranmu aka buɗe makarantu ba – Gwamnatin tarayya

38
0

Gwamnatin tarayya, ta ce ba ta goyon bayan sake bude makaratun da aka yi a ranar 18 ga watan Janairu.

A lokacin jawabin kwamitin shugaban kasa akan cutar Covid-19, Ministan Ilimi Adamu Adamu ya ce, gwamnatin tarayya da gwamnatocin jahohi ba su samu daidaito ba  akan bude makarantun.

Adamu, wanda ya bayyana cewa kwamitin na PTF zai ci gaba da sa ido kan yanayin yaduwar cutar a kullum, sannan kuma akwai yiwuwar sake yin bita kan komawar makarantun.

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin PTF, Boss Mustapha, ya ce za a sake bitar bude makarantun saboda yawaitar karuwar masu kamuwa da cutar a kullum, da kuma kalubalen da ake fuskanta wajen magance ta, musamman samar da iskar shaka.

Mustapha ya yi gargadi ‘yan Nijeriya su hada kai da PTF domin gujewa sake sanya dokar kulle a fadin kasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply