Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya caccaki gwamnatin Nijeriya kan sha’anin tsaro, inda yace babu gaskiya a lamarin kwata-kwata.
Wike da ya yi magana a gidan talabijin na Channels yace gwamnatin ta siyasantar da lamarin tsari a kasar.
Yace idan ka tambayi kanka, game da sha’anin tsaro a Nijeriya, amsar da zaka ba kanka ita ce babu tsaro ta ko ina.
