Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi “Ba hannuna a karkatar da kudin ciyar da ‘yan makaranta” – Sadiya

“Ba hannuna a karkatar da kudin ciyar da ‘yan makaranta” – Sadiya

379
0

Ma’aikatar jin kai da kare bala’o’i ta Nijeriya ta nisanta kanta daga zargin karkatar da kudaden ciyar da ‘ yan makaranta da hukumar ICPC ta bankado.

A wata sanarwa daga mataimaki na musamman kan kafafen watsa labarai na ministar, Nneka Ikem Anibeze, ta ce shirin ciyar da daliban kwalejojin gwamnatin tarayya, ya sha bamban da na ‘yan firamare da ake zargin badakalar.

Takardar ta ce shirin ciyar da daliban kwalejojin gwamnatin tarayya ba ya karkashin ma’aikatar.

Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa ICPC dai ta ce ta bankado wasu kudade da aka karkatar bilyan 2.67 da aka ware don ciyar da ‘yan makaranta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply