Home Labarai Ba kanshin gaskiya a labarin yin watsi da alhazan Kano – inji...

Ba kanshin gaskiya a labarin yin watsi da alhazan Kano – inji NAHCON

72
0

Daga Abdullahi Garba Jani

Hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya -NAHCON- ta musanta rahotannin da ake yadawa a kafar sadarwar soshiyal midiya cewa ta yi fatali da wasu maniyyata aikin hajjin bana kimanin 400 da suka yi rajistar zuwa aikin hajji ta jihar Kano.

Da ya ke ganawa da ‘yan jarida don maida martani kan zarge-zargen, kwamishinan hukumar mai kula da aikace-aikace, Malam Abdullahi Saleh, ya ce hukumar ba ta yi kasa a guiwa ba wajen ganin kowane Alhaji ya samu kyakkyawar kulawa a aikin hajjin wannan shekara.

Sai dai bata nuna ba, amma ta yi shudi, inda ya ce akwai alhazan da suka yi rajista ta jirgin yawo wadanda ba su samu kyakkyawar kulawa ba wanda ba hakkinsu bane.

Malam Abdullahi yace an yi jigilar dukkanin alhazai 44,450 da suka yi rajista ta hukumomin kula da aikin hajji na jihohi kafin a rufe filin jirgin saman Saudiyya a ranar 4/08/2019.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply