Ministan sufuri Mr Rotimi Ameachi ya bayyana cewa kudade ba su ne kalubalen jinkirin da ake samu ba wajen kammala aikin layin dogo da ya taso daga birnin Lagos zuwa Ibadan ba.
Ministan wanda ya bayyana haka ne ya yin da ya kai ziyarar duba aikin, ya ce kada ‘yan kwagilar su fake da annobar coronavirus wajen kin yin hanzari ya yin gudanar da aikin.
A karshe ya umurci ‘yan kwagilar da su kammala aikin nan da watanni 5 masu zuwa.
