Home Sabon Labari Ba lallai Tierney da Thomas su buga wasan Arsenal da Benfica ba

Ba lallai Tierney da Thomas su buga wasan Arsenal da Benfica ba

28
0

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta, ya bayyana halin da ‘yan wasansa Thomas Partey da Kieran Tiarney wanda ke jinyar raunika ke ciki, a daidai lokacin da kungiyar tasa ke shirin karawa da Benfica a filin wasa na Stadio Olimpico da ke Birnin Roma, a wasan zagayen ‘yan 32 da za a yi a ranar Alhamis.

Arteta a ya ce ba ya da tabbacin dawowar ‘yan wasan nasa a ranar Alhamis, saidai ya ce Tierney na da babbar damar shida tawagar ‘yan wasan da za su fafata a wasan.

Partey da Tierney ba su sami buga wasan Firimiyar da kungiyar ta yi nasara kan Leed da ci 4-2 a ranar Lahadi saboda raunin da suke da shi.

Da yake bayani kan ‘yan wasan guda biyu bayan kammala wasan na jiya, Arteta ya ce babu tabbacin ‘yan wasan za su iya buga wasan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply